Share the post "OKA ta nemi Majalisar Kano ta binciki tsohon Mataimakin Gwamna kan zargin karkatar da Naira miliyan 308"
Wata Kungiya mai rajin samar da ci gaba mai ma,ana a Jihar Kano (One Kano Agenda) ta shigar da korafi a gaban Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano tana neman majalisar ta binciki zargin karkatar da Naira miliyan 308 da tsohon Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya yi.
Kungiyar ta bayyana a cikin korafin da Shugabanta, Ambasada Abbas Abdullahi Yakasai ya sanya hannu cewa korafin ya samo asali ne daga wani bayani da Mai Bai wa Gwamnan Kano Shawara kan Ilimin Tsangaya, Sheikh Musa Falaki ya yi, inda ya zargi tsohon Mataimakin Gwamnan da karkatar da fiye da Naira miliyan 300 da aka ware wa malamai domin addu’o’i na tsawon watanni bakwai.
A cikin korafin, OKA ta ce:
Mun rubuto ne a madadin One Kano Agenda domin jan hankalin Majalisar Dokokin Jihar Kano kan zargin karkatar da kudaden jama’a da aka ware domin shirye-shiryen addu’o’i na musamman a kananan hukumomi 44 na jihar.”
An ce kowace Karamar hukuma ta bayar da Naira miliyan 44 a kowane wata na tsawon watanni bakwai domin gudanar da addu’o’i na musamman a fadin jihar, karkashin jagorancin Sheikh Musa Falaki da Sheikh Ibrahim Sheshi Maihula. Sai dai malaman sun bayyana cewa ba su karbi kudi ba kuma ba su gudanar da addu’o’in da aka ce an ware kudin ba.
Kungiyar ta nemi Majalisar ta:
1. Gudanar da cikakken bincike kan zargin karkatar da kudin da aka ware wa shirye-shiryen addu’o’i.
2. Gayyatar dukkan masu ruwa da tsaki ciki har da tsohon Mataimakin Gwamna, Alhaji Aminu Abdussalam Gwarzo, jami’an ALGON, Sheikh Musa Falaki, Sheikh Ibrahim Sheshi Maihula, da hukumar yaki da cin hanci ta Kano.
Karanta Labari: Mataimakin Gwamnan Kano ya yaba da rawar CRC wajen inganta rayuwar al’umma
3. Tantance adadin kudin da aka ware da kuma yadda aka amince da su, aka raba su, da yadda aka yi amfani da su.
4. Ba da shawarar matakan shari’a ko na gudanarwa idan an tabbatar da laifi.
5. Tabbatar da dawo da duk wani kuɗin jama’a da aka karkatar bisa doka.
Karanta Labari: Shekaru 100 da Tallar Tsintsiya: Labarin Dattijon Bauchi da Bai Gaji da Neman Halal Ba
Kungiyar ta jaddada cewa ba ta yi korafin domin hukunta wani ba, sai dai neman gaskiya, adalci da bin doka domin kare amincin cibiyoyin gwamnati da kuma tabbatar da sahihancin shugabanci.
Share the post "OKA ta nemi Majalisar Kano ta binciki tsohon Mataimakin Gwamna kan zargin karkatar da Naira miliyan 308"









