Share the post "Kano: Hukumar Kashe Gobara ta Kano Ta Fitar da Jadawalin Rahotannin Ayyukanta na Watan Yuni"
Daga Rahma Ibrahim Zubairu Dambatta
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta fitar da rahoton ayyukanta na watan Yunin 2026, inda ta bayyana cewa ta amsa kiran gaggawa guda 30 da suka shafi gobara a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.
Karanta Labari: Faifan Dala: Tsohon Sakataren Yada Labarai na Ganduje, Anwar, Ya Janye Bayanan Shaidarsa Akan Ja’afar Ja’afar
Rahoton ya nuna cewa an gudanar da ayyukan ceto guda bakwai, yayin da aka samu kira daya na karya.
Rahoton ya kuma bayyana cewar duk da kokarin jami’an hukumar, mutane biyar sun rasa rayukansu, yayin da aka yi nasarar ceto mutane uku daga hadura daban-daban.
Karanta Labari: Shekaru 100 da Tallar Tsintsiya: Labarin Dattijon Bauchi da Bai Gaji da Neman Halal Ba
Hukumar ta ce gobara ta lalata kadarori da darajarsu ta kai ta sama da naira miliyan 120, yayin da aka yi nasarar ceto kadarori da darajarsu ta kai sama da naira miliyan 481 ta hanyar kai dauki cikin lokaci.
Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, , ya bukaci al’umma su rika yin taka-tsantsan wajen amfani da wuta tare da tabbatar da kashe ta gaba daya bayan an gama amfani da ita.
Haka kuma, ya shawarci iyaye da masu kula da yara su hana su wasa a kusa da tafkuna, koramu, koguna da rijiyoyin da ba a rufe ba domin kare su daga hadarin nutsewa.
Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Saminu Yusuf , ya ce hukumar za ta ci gaba da ba da agajin gaggawa cikin hanzari da kuma wayar da kan al’umma kan matakan kare rayuka da dukiyoyi.
Share the post "Kano: Hukumar Kashe Gobara ta Kano Ta Fitar da Jadawalin Rahotannin Ayyukanta na Watan Yuni"









