Babbar Kotun Kano ta Hana Hanga Wallafa Kalaman Batanci

0

Babbar Kotun Jihar Kano, karkashin jagorancin Mai Shari’a Jamilu Shehu Suleman, ta bayar da umarnin wucin gadi na hana Muhammad Samir Rufa’i Sani Hanga daga wallafa ko yada kalaman batanci da ake zarginsa da yi kan Isa Ado Maidoya a dandalin Facebook ko kuma duk wasu kafafen sada zumunta.

Wanda ake tuhuma shi ne dan Sanata mai wakiltar Kano Municipal a Majalisar Dattawa, Hon. Rufa’i Sani Hanga.

Wannan hukunci ya biyo bayan bukatar gaggawa da Lauyan Maidoya ya shigar a ranar 3 ga Yuli, 2026, tare da rantsuwar shaidu mai sakin layi 21 da kuma wasu hujjoji.

Karanta Labarai: Kotu ta yanke hukuncin kisa ga wanda ya yi satar wayar Samsung da kuma kisan kai

Bayan sauraron hujjojin da Barrister Faruk Muhammad, lauya ga mai kara ya gabatar, kotu ta umarci wanda ake tuhuma, wakilansa, abokansa, ko duk wani da yake aiki a madadinsa, da su daina yin wallafa a kan mai kara a yanar gizo har sai an yanke hukunci kan babbar bukatar da aka shigar.

Karanta Labari: Hukumar Shari’a ta Kano ta Ladabtar da Alkalai da Ma’aikatan Kotuna Bisa Laifin Cin Hanci da Rashawa

Karar da aka shigar karkashin lamba No. K/650/2026, an dage zaman zuwa ranar 30 ga Yuli, 2026 domin ci gaba da sauraro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here