Share the post "Yan Sanda Sun Ceto Ma’aikacin INEC da Aka Sace a Zamfara "
Daga Rahma Ibrahim Zubairu Dambatta
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta ce ta ceto wani ma’aikacin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da aka sace, tare da dakile wasu hare-haren ‘yan bindiga da kuma kwato daruruwan shanun da aka sace a kananan hukumomin Talata Mafara, Gummi da Gusau.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce ‘yan bindiga sun kai hare-hare a yankunan da abin ya shafa, inda suka sace shanu da kuma wani ma’aikacin INEC da ke kan aikin hukuma tare da Hukumar Shirya Jarabawar NECO.
Karanta Labari: Yaro Mai fatan Zama Dan Jarida Ya Rasu a Ramin Diban Yashi a Kano
Ya ce bayan samun bayanan sirri, jami’an ‘yan sanda tare da dakarun soji sun kai farmaki maboyar ‘yan bindigar a Dajin Gando, inda suka ceto mutanen da aka sace ba tare da sun ji rauni ba, tare da kwato daruruwan shanun da aka sace aka mayar wa masu su.
A wani samame da aka kai a Kwanar Ganuwa da ke Karamar Hukumar Gusau, jami’an tsaro sun kuma ceto matafiya da manoman da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su, yayin da maharan suka tsere zuwa cikin daji.
Karanta Labari: Raina Kotu: Mataimakin Kwamishinan Yansanda Na Fuskantar Hadarin Daurin Kurkuku
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, CP A. M. Bello, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da hare-hare domin kawar da ayyukan ta’addanci da sauran laifuka a fadin jihar.
Share the post "Yan Sanda Sun Ceto Ma’aikacin INEC da Aka Sace a Zamfara "









