Manoma a Garun Gundutse Sun Roki Gwamnatin Kano Ta Sanya Ido Kan Kwace Gonakinsu

0

Al’ummar Garun Gundutse da ke Karamar Hukumar Kura, Jihar Kano, sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta sanya ido tare da gudanar da bincike kan batun kwace gonakinsu da ke Kwarin Dangana. Manoman sun bayyana cewa gonakin da ake amfani da su wajen noman rani da damina an kwace su ne da sunan fadada gidan ruwan Tamburawa, amma daga bisani ma’aikatan da ke gudanar da aikin sun fara amfani da wuraren wajen dibar yashi domin sayarwa.

Karanta Labari: Rusau: Mun bi Ka’idojin Da Suka Kamata, Inji Masu Filayen Sharada, Sun Roki Gwamna Abba Ya Kawo Dauki

A cewar wani mai magana da yawun manoman, Abdullahi Abubakar ya ce gonakin da aka kwace sun kunshi bishiyoyin mangwaro da amfanin gona daban-daban, kuma ba a biya su ko sisin kwabo ba.

Yace sun kiyasta asarar da suka yi a yanzu ta kai dubban naira. Hakan ya jefa su cikin matsin tattalin arziki da rashin tabbas ga rayuwarsu.

Karanta Labari: Babbar Kotun Jigawa ta bayar da umarnin wucin gadi kan Wasu filaye a Hadejia

Wakilinmu, Dantala Uba Nuhu Kura, ya ruwaito cewa manoman sun bayyana zargin cewa ma’aikatan aikin suna mayar da wuraren da aka kwace hannun jari, inda suke dibar yashi daga rafin da ke wurin, sannan suna sayar da shi ga wasu al’umma ba tare da sanin manoman ba.

Manoman sun roki Gwamnatin Jihar Kano da ta kawo musu daukin gaggawa, tare da tabbatar da adalci a cikin wannan lamari.

Sun bukaci a biya su diyya bisa asarar da suka yi, sannan a dakatar da duk wani amfani da wuraren da ba bisa ka’ida ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here