Share the post "Raina Kotu: Mataimakin Kwamishinan Yansanda Na Fuskantar Hadarin Daurin Kurkuku"
Babbar Kotun Jihar Kano, karkashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Mahmoud ta gargadi Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda (ACP) Babagana Bdukar na Hedikwatar Shiyya ‘Yan Sanda dake Kano, saboda kin bin umarnin kotu.
Karanta Labari: Hukumar Shari’a ta Kano ta Ladabtar da Alkalai da Ma’aikatan Kotuna Bisa Laifin Cin Hanci da Rashawa
Alkalin ta yi gargadin cewa ci gaba da kin bin umarnin kotu, na iya zama raina kotu, kuma babban laifi ne da zai iya kaiwa ga daurin kurkuku.
Asalin Shari’ar
Shari’ar ta samo asali ne daga rikici akan gidan No. QA-270 da ke Fanisau a Karamar Hukumar Ungogo, Jihar Kano.
Tunda fari Mai kara, Abba Shittu Sharubutu, ya shigar kara a gaban Babbar Kotun Jihar Kano karkashin jagorancin Yusuf Ubale da bukatar gaggawa a watan Afrilu 2026 kan wasu mutane da suka hada da: Isiyaku Auwalu (wanda aka fi sani da Dan Kwangila), Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya, AIG Shiyya ta 1 dake Jihar Kano, ACP Babagana Bukar da kuma Sufeto Dauda Usman (IPO).
Bayan sauraron bayanan lauyan mai kara, Barrister Muhammad Kelechi Nwabueze, Mai Shari’a Ubale ya bayar da umarnin wucin gadi cewar dukkan bangarorin su ci gaba da tsayawa a yadda suke har sai an yanke hukunci kan bukatar da aka shigar.
Karanta Labari: Babbar Kotun Kano ta Hana Hanga Wallafa Kalaman Batanci
Amma duk da wannan umarnin sai aka yi zargin cewar ACP Bukar yayi amfanin da karfi wajen fitar da mutanen dake zaune a gidan da ake shari’a a kansa
Mai Shari’a Mahmoud ta kuma umarta cewa a mika takardun shari’a ta hannun Jami’an ‘yan sanda kafin ranar da aka dage shari’ar.
Mai shari’a Aisha Mahmoud ta nuna damuwa matuka cewa ACP Bukar bai bi umarnin kotu ba.
Ta jaddada cewa rashin bin umarnin kotu yana rage darajar kotu, kuma ya yi gargadin cewa irin wannan raini na iya kaiwa ga shigar da karar raina kotu.
“Rashin bin umarnin wannan kotu ba za a lamunta ba. ACP Babagana Bukar na iya fuskantar ɗaurin kurkuku saboda raina kotu idan ya ci gaba da yin watsi da umarni,” in ji alkalin.
An dage shari’ar zuwa ranar 13 ga Watan Yuli, 2026 don sauraron bukatar da aka shigar.
A halin yanzu, kotu ta bayyana a fili cewa duk wani kara raina umarninta zai jawo mummunan sakamako, ciki har da daurin wanda ya yi rainin.
Share the post "Raina Kotu: Mataimakin Kwamishinan Yansanda Na Fuskantar Hadarin Daurin Kurkuku"









