Yan Sanda a Zamfara sun cafke wanda ake nema a Akwa Ibom

0

Daga Rahma Ibrahim Zubairu Dambatta

Rundunar ‘Yan Sanda ta Kasa reshen Jihar Zamfara ta kama wani mutum da ake nema ruwa a jallo, wanda ya tsere daga Jihar Akwa Ibom domin kauce wa fuskantar shari’a.

A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar Yansandan Jihar Zamfara DSP Yazid Abubakar, ya fitar, ya bayyana cewa ingantattun  bayanan sirri sun nuna cewa wanda ake zargin, Nura Bala mai shekaru 41, ya aikata wani laifi a Jihar Akwa Ibom kafin ya tsere zuwa Jihar Zamfara.

Bayan samun bayanan, rundunar ta fara gudanar da bincike cikin gaggawa, lamarin da ya kai ga nasarar cafke shi.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, CP Ahmad Muhammad Bello, ya tabbatar da cewa za a mika wanda ake zargin ga Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Akwa Ibom domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu kan zarge-zargen da ake masa.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta yaba da kyakkyawar hadin gwiwar da ke tsakanin rundunonin ‘yan sanda na jihohi daban-daban, tana mai bayyana cewa wannan nasara ta nuna irin muhimmancin hadin kai wajen yaki da aikata laifuka da tabbatar da adalci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here