Share the post "Yaro Mai fatan Zama Dan Jarida Ya Rasu a Ramin Diban Yashi a Kano"
Daga wakilinmu
A Unguwar Gidan Kara Getsi, yankin Karamar Hukumar Ungogo dake Jihar Kano, al’umma sun shiga cikin damuwa bayan rasuwar wani yaro mai shekaru 13, Abdullahi Ibrahim Gama, wanda ke da burin zama dan jarida nan gaba.
Karanta Labari: Tsohon Karfen Layin Dogo Da aka Bari a titi ya Zama Barazana ga rayukan Jama’a a Kano
Yaron ya gamu da ajalinsa a ramin da ake kwasar yashi, sakamakon ruwan sama da ya taru a wurin.
Mazauna yankin sun bayyana cewa matsalar ta samo asali ne daga ayyukan masu kwasar yashi da ba sa bin ka’ida.
Wannan ya janyo zaizayar kasa da hadarin da ya yi sanadiyyar mutuwar yara biyu.
Muhammad Abubakar da Ubale Muhammad, wadanda suka yi magana a madadin Kungiyar matasan yankin, sun ce duk da ayyukan raya kasa da gwamnati da Bankin Duniya ke yi, masu kwasar yashi sun ki bayar da hadin kai, wasu batagari suna amfani da wuraren a matsayin mafaka ga masu fataucin miyagun kwayoyi.
Karanta Labari: Yadda Gobarar Tankokin Mai Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane Da Dama A Zariya
Ubale ya kara da cewa, masu fataucin kwayoyi sun mayar da yankin tamkar kasuwa, abin da ke barazana ga tsaron al’umma.
Bola da aka bari a ramukan ya janyo yara suna kunna wuta, hayakin da ke cutar da masu asma da sauran marasa lafiya.
Karanta Labari: Babbar Kotun Kano ta Hana Hanga Wallafa Kalaman Batanci
Al’umma sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano, Hukumar NDLEA, da kwamitin tsaro na jihar da su kawo dauki.
Sun kuma roki a dakatar da ayyukan kwasar yashi ba bisa ka’ida ba, tare da samar da tsaro da tsaftar muhalli domin kare rayukan jama’a.
A karshe, mazauna Unguwar Gidan Kara Getsi sun mika sakon ta’aziyya ga iyalan da suka rasa ‘ya’yansu, musamman iyalan Abdullahi Ibrahim Gama, wanda burinsa na zama dan jarida ya tsaya cak sakamakon wannan iftila’i.
Share the post "Yaro Mai fatan Zama Dan Jarida Ya Rasu a Ramin Diban Yashi a Kano"









