Hukumar Shari’a ta Kano ta Ladabtar da Alkalai da Ma’aikatan Kotuna Bisa Laifin Cin Hanci da Rashawa

3

Daga Rahma Ibrahim Zubairu Dambatta

Hukumar Kula da Ma’aikatan Shari’a ta Jihar Kano ta dauki matakan ladabtarwa kan wasu alkali da ma’aikatan kotuna bayan taronta na 90 da aka gudanar a ranar 3 ga Yuli, 2026.

Hukumar ta tilasta wa Alkali Aliyu Yahaya Muhammad ritaya bisa samunsa da laifin karɓar cin hanci, tare da umarce shi da ya mayar da Naira dubu 250.

Haka kuma, an dakatar da magatakardan kotun, Ibrahim Ahmad Ibrahim, ba tare da albashi ba na tsawon watanni huɗu saboda hannu a lamarin.

Hakazalika, an tilasta wa Mukaddashin Daraktan Yada Labarai da Kididdiga na Kotun Daukaka Kara ta Shari’a, Muzambilu Ado, ritaya saboda rashin daidaito a takardun karatunsa.

Har ila yau, Hukumar ta rage wa Alkali Usman Haruna Usman matsayi da mataki guda saboda sakaci, yayin da ta yi wa Alkali Abdu Abdullahi Wayya gargadi kan gazawa wajen sa ido kan tsarin bayar da beli.

Labari: Kudin Marayu: Yan Sanda Sun Kama Ma’aikacin Kotu Saboda Zargin Wawure Naira Milyan 35

Mai magana da yawun Hukumar Shari’ar Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya ce Hukumar ba za ta lamunci cin hanci, rashawa ko rashin da’a ba, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukuncin da ya dace.

3 COMMENTS

  1. Matakin da yakamata ace ana dauka kenan duk wanda aka kama da cin hanci da rashawa a hukuntashi hakan zaisa a samu raguwar aikata laifin Allah yasa mudace

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here