Mataimakin Gwamnan Kano ya yaba da rawar CRC wajen inganta rayuwar al’umma

0

Daga Idris Muhammad Dawakin Kudu

Mataimakin Gwamnan Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya bayyana kwamitin wayar da kan jama’a da tallafawa ilmi wato CRC a matsayin muhimmiyar kafa da ke taimakawa wajen aiwatar da ayyukan ci gaban al’umma a fadin jihar.

Karanta Labari: Hadakar Kungiyar Lauyoyi Mata ta Caccaki Gwamnatin Kano kan Matsalar Tsaro

Ya bayyana hakan ne yayin da shugabannin kwamitin na CRC daga kananan hukumomi 44 na jihar nan suka kai masa ziyarar taya murna kan hawansa mukamin Mataimakin Gwamna tare da gaisuwar Babbar Sallah.

Sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na Ofishin Mataimakin Gwamnan, Rilwanu Idris Malikawa ya fitar ta ce Alhaji Murtala Garo ya yaba wa gudummawar da kwamitin ke bayarwa a fannoni da suka hada da ciyar da dalibai abinci, gyaran makarantu, tallafawa ilimin yara kanana, gyaran asibitoci da ayyukan samar da ruwa.

Ya kuma tabbatar musu da cewa zai isar da bukatunsu ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da daukar matakan da suka dace domin magance matsalolin da suke fuskanta.

Tun da farko, Shugaban kwamitin na CRC na Jihar Kano, Alhaji Shakoor Yassar, ya ce sun kai ziyarar ne domin taya Mataimakin Gwamnan murna tare da gode wa gwamnatin jiha bisa goyon bayan da take bai wa kwamitin.

Wakilinmu na Ofishin Mataimakin Gwamna, Idris Muhammad Dawakin Kudu ya rawaito cewa, daga nan Alhaji Shakoor Yassar ya bukaci gwamnatin ta ci gaba da tallafawa kwamitin domin kara inganta ayyukansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here