Share the post "Dalilin Da Ya Sa Taron Tsaro Na NUJ Ya Ke Da Muhimmanci Ga Ci Gaban Kasa"
Daga Abbas Ibrahim
Yayin da Najeriya ke ci gaba da fama da matsalolin tsaro masu rikitarwa daga ta’addanci da ‘yan fashi zuwa laifukan yanar gizo, rikice-rikicen al’umma da yada labaran karya, abu daya ya bayyana: ba jami’an tsaro ko kafafen yada labarai za su iya cika rawar da ke kansu su kadai ba tare da haɗin gwiwa ba.
Saboda haka, Kungiyar Yan Jarida ta Kasa (NUJ) za ta gudanar da Taron Tsaro na Kasa a Abuja a ranakun 18 da 19 ga Yuni, 2026, karkashin taken, “Kafafen Yada Labarai da Jami’an Tsaro a Matsayin Abokan Hulda Wajen Gina Kasa.” Wannan taro dama ce ta tattauna muhimmin alaka da ake yawan fahimta ba daidai ba a tafiyar dimokuradiyyar Najeriya.
Tsawon shekaru, Hulda Yan jarida da hukumomin tsaro ta kasance cike da zargi, tashin hankali da kuma rikici lokaci-lokaci. Yan jarida sun sha zargin jami’an tsaro da hana samun bayanai, tsoratar da ma’aikatan kafafen yada labarai da kuma tauye ‘yancin fadar albarkacin baki. A gefe guda, jami’an tsaro sukan nuna damuwa cewa wasu rahotannin kafafen yada labarai na iya lalata ayyuka, fallasa bayanan sirri ko kuma kara karfafa barazanar tsaro.
Wannan rashin fahimtar juna ya haifar da rashin amincewa wanda ya kan hana ingantaccen sadarwa musamman a lokacin rashin jituwa. Daga yakin da ake yi da ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas zuwa martani ga tarzoma da rikice-rikicen al’umma, rashin jituwa kan yadda ake sarrafa bayanai ya kan shafi burin da duka bangarorin ke da shi: kare kasa da tsaron ‘yan kasa.
Karanta Labari: NUJ Kano Ta Jajanta Wa Iyalin Marigayiya Hadiza Mai Abinci
An tabbatar da cewa ba za a iya samun tsaro mai dorewa ba tare da amincewar jama’a ba, kuma amincewar jama’a ba za ta tabbata ba tare da sahihan bayanai ba. A nan ne kafafen yaɗa labarai ke da muhimmanci.
Kafafen yada labarai na zama gada tsakanin gwamnati da jama’a, suna sanar da ‘yan kasa, gano barazanar da ke tasowa, inganta daukar alhakin shugabanni da kuma yaki da yada labaran karya. A gefe guda, jami’an tsaro na da nauyin kare rayuka, kare ikon kasa da kuma tabbatar da doka da oda. Duk da bambancin ayyukansu, burinsu daya ne: Najeriya mai zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba.
Karanta Labari: Farfesa Aliyu Ga ’Yan Jarida: Ku Guji Dogaro da AI, Ku Karfafa Kwarewa da Ka’ida
A wannan zamani na dijital inda labaran karya ke yaduwa cikin sauri fiye da gaskiya, hadin gwiwa tsakanin Yan jarida da jami’an tsaro ya zama dole fiye da da. Ingantaccen haɗin gwiwa zai taimaka wajen yaki da yada labaran karya, kara wayar da kan jama’a, tallafa wa kokarin hana rikici da kuma karfafa karfin kasa wajen fuskantar barazanar tsaro.
Saboda haka, Taron Tsaro na Kasa na NUJ ba taro na yau da kullum ba ne. Wuri ne na tattaunawa cikin gaskiya, fahimtar juna da kuma gina sabuwar amincewa tsakanin waɗannan muhimman cibiyoyi guda biyu.
Taron zai haɗa Yan jarida, kwararrun tsaro, masu tsara manufofi da sauran masu ruwa da tsaki, inda ake sa ran samar da dabarun aiki don inganta rabon bayanai, kare ‘yancin kafafen yada labarai, karfafa dabi’un aiki da kuma inganta rahotanni masu ɗaukar nauyi kan batutuwan tsaro.
Gina kasa na bukatar cibiyoyi masu karfi da ke aiki tare don cimma buri ɗaya. Duk da cewa kafafen yada labarai da jami’an tsaro na iya kallon kalubalen kasa daga bangarori daban-daban, dukansu abokan hulda ne da ba za a iya yi ba tare da su ba wajen kare dimokuradiyya, inganta zaman lafiya da kuma tabbatar da makomar Najeriya.
Shugaban NUJ, Kwamared Alhassan Yahya, ya bayyana da fata cewa:
“Lokacin da mahalarta suka taru a Abuja, ana sa ran taron ba zai tsaya kan matsalolin da ake da su ba kawai, sai dai ya tsara sabuwar hanya ta hadin gwiwa mai inganci, bisa girmama juna, kwarewa da kuma sadaukarwa ga muradun kasa.”
“A wannan lokaci da Najeriya ke fuskantar sabbin kalubalen tsaro, karfafa haɗin gwiwa tsakanin kafafen yada labarai da jami’an tsaro ba zabi ba ne, wajibi ne na dabarun ci gaban ƙasa.” In ji Ƙwamared Yahya.
Shugabar kwamitin shirya taron, kuma Mataimakiyar Shugabar Kungiyar NUJ, Dr Abimbola Oyetunde ta ce:
“A karshe taron, ana sa ran mahalarta za su amince da sanarwar aiki da kuma tsara tsarin da zai jagoranci hadin gwiwa a nan gaba tsakanin kafafen yada labarai da hukumomin tsaro.”
Da shirye-shiryen da aka yi zuwa yanzu, taron zai yi nasara, in Allah ya so. Domin kuwa, “Jami’an tsaro da kafafen yada labarai sukan fi karfi idan suna aiki tare wajen kare muradun jama’a.”
Abbas Ibrahim ya rubuta daga Kano kuma za a iya tuntubar sa ta [email protected]
Share the post "Dalilin Da Ya Sa Taron Tsaro Na NUJ Ya Ke Da Muhimmanci Ga Ci Gaban Kasa"









