Share the post "Farfesa Aliyu Ga ’Yan Jarida: Ku Guji Dogaro da AI, Ku Karfafa Kwarewa da Ka’ida"
Daga Abubakar Adamu
Kungiyar ‘Yan jarida masu amfani da Kafafen Sadarwa na Zamanin, (Online) reshen Kano ta horas da ‘ya’yanta dabarun sanin makamar aiki.

Yayin gabatar da kasida kan amfani da Fasahar AI a aikin jarida, Farfesa Rukayya Yusuf Aliyu daga Jami’ar Bayero Kano ta yi kira ga ’yan jarida da kada su dogara kacokan ga fasahar AI wajen samar da labarai.
Ta bayyana cewa duk da amfaninsa, Fasahar AI na iya samar da bayanan da ba daidai ba, don haka, a cewarta ya kamata a yi amfani da fasahar domin inganta aiki da taimako kawai.

Farfesa Aliyu ta jaddada muhimmancin bin ka’idojin aikin jarida, musamman tabbatar da sahihancin tushe da gaskiyar bayanai kafin wallafawa.
Karanta Labari: Jami’an Tsaro Sun Dakile Yunkurin Tayar da Zaune Tsaye a Kano Bayan Taron Sulhu

Haka kuma, ta karfafa ’yan jarida da su ci gaba da sabunta iliminsu tare da bin sabbin hanyoyin zamani, maimakon dogaro da AI ko wasu kafafen sadarwa kadai.
Ta bayyana cewa masana harshen Hausa na aiki tukuru wajen kirkirar tsarin fassarar Hausa daidaitacciya domin magance kurakuran da fasahar AI ke haifarwa wajen fassara.
A nasa jawabin, Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya, ya sake jaddada muhimmancin kafafen yada labarai a gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ya yi alkawarin ci gaba da hadin gwiwa da ’yan jarida tare da samar da yanayi mai kyau ga ayyukan kungiyar.
Haka kuma, Babban Daraktan Yada Labarai na fadar Gwamnatin. kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya nuna jin dadinsa da ci gaban kungiyar, inda ya bayar da gudummawar naira miliyan biyu (N2m) domin tallafa wa ayyukanta.
Karanta Labari: Rikicin RTEAN Kano Ya Kare Bayan DSS ta Jagoranci Zaman Sulhu
Shugaban Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kano, Kwamared Sulaiman Abdullahi Dederi, wanda Ma,ajin Kungiyar Kwamared Nura Bala Ajingi ya wakilta ya bukaci mahalarta da su kiyaye ka’idojin aikin jarida tare da ci gaba da neman karin ilimi.
Ya tabbatar musu da cikakken goyon bayan Kungiyar domin cimma nasarori masu ma’ana.
Tun da farko, Shugaban kungiyar, Kwamared Abubakar Abdulkadir Dangambo, ya bayyana cewa kungiyar za ta ci gaba da shirya irin wadannan taruka don kara wa ‘ya’yanta kwarewa a aikinsu.
Share the post "Farfesa Aliyu Ga ’Yan Jarida: Ku Guji Dogaro da AI, Ku Karfafa Kwarewa da Ka’ida"









