Jami’an Tsaro Sun Dakile Yunkurin Tayar da Zaune Tsaye a Kano Bayan Taron Sulhu

0

Daga Usman Idris

Jami’an Rundunar tsaro da kare Gandun Daji na jihar Kano sunyi nasarar dakile wani yunkurin matasan unguwar Tudun Fulani sa’ilin da suka fito da yammacin jiya Lahadi dauke da muggan makamai suna kwacen wayoyi da tayar da hankalin jama’a, awanni kadan bayan taron baka da baka da akace dattawan yankin sunyi dasu don ganin sun ajiye makamansu sun rungumi zaman lafiya.

Usman Abdullahi Umar shine jami’in hulda da jama’a na rundunar tsaro da kare Gandun daji ta jihar Kano ya tabbatar da wannan nasara da jami’an nasu suka samu ta fatattakar masu neman tayar da zaune tsaye a Unguwar, Kurna Tudun Fulani dake Yankin Karamar Hukumar Dala a jihar Kano.

Karanta Labari: A yi amfani da zaman sulhu maimakon karfi domin dakile matsalar shaye-shaye da ‘yan daba a Kano – A.A Zaura

Wadanda ake zargin da neman tayar da zaune tsayen da suka hadar da Jabir Tudun Fulani, Aliyu Aliyu, 22, Salisu, 20, da suka zanta da wakilinmu sun musanta zargin da ake yi musu.

Wannan aikin kakkabe bata garin na hadaka an yi shi ne karkashin Ofishin Mataimakin Shugaban Rundunar Tsaro da Kare Gandun Daji ta kasa reshan jihar Kano mai kula da aiyuka na musamman ACNF Alhaji Mansur.

Wanda daga bisani Usman Abdullahi Umar jami’in hulda da jama’a na rundunar tsaron ya roki Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya baiwa rundunar gudunmawar motoci da kayan aiki, yana mai bayyana cewa, “dazarar sun samu wadannan kayayyaki da suka nema, za su kunna kai dazukan Shanono da Bagwai da Ghari da Tsanyawa da Doguwa da sauran Dazukan dake kewaye da Kano domin ragargazar duk wani mai neman ya hana jihar zaman lafiya ko kawo mata barazana irinta tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here