An yi karar Sarkin Rano da Karamar Hukumar Bunkure kan zargin kwace gonaki 27 a Gafan

0

Babbar Kotun Jihar Kano ta dage zamanta domin fara sauraron shari’ar rikicin wasu filaye da gonaki a Gafan, Karamar Hukumar Bunkure har zuwa ranar 9 ga Yuli, 2026.

Karanta Labari: Hukuncin Kisa: Kotun Daukaka Kara Ta Gargadi Abduljabar Kan Muhimmancin Lauya a Shari’arsa

Inusa Alasan da wasu mutane 26 ne suka shigar da karar, suna rokon kotun da ta hana Sarkin Rano, Alhaji Muhammad Isah, Karamar Hukumar Bunkure, Kamfanin Syno Hydro Trimming, Ado Alasan da kuma wasu mutane tara da suke zargin zasu kwace musu gonaki 27 da ke Gafan, Karamar Hukumar Bunkure, a Jihar Kano.

Masu karar sun ce sun gaji gonakin ne daga iyayensu kuma suna da shaidar mallakarsu tun shekaru da dama.

Justice Watch Hausa ta ruwaito cewa tuni a ranar 29 ga Afrilu, Mai Shari’a Nasiru Saminu ya bayar da umarnin wucin gadi da ya hana wadanda ake kara shiga, noma, sayarwa, haya, jingina, ko yin wata mu’amala da gonakin har sai an yanke hukunci kan bukata da aka shigar.

Karanta Labari: Kotu ta yanke hukuncin kisa ga wanda ya yi satar wayar Samsung da kuma kisan kai

Umarnin ya kuma hana su fara gini ko dora wani tsari a kan kasar da ake rikici a kanta.

A yayin zaman kotun da aka yi ranar Laraba, lauyoyi sun shaida wa kotu cewa ba a kammala isar da takardu ga dukkan bangarorin ba.

Lauyan masu kara, Barrister Abubakar Tijjani Bebeji, ya bayyana wa Justice Watch News Hausa cewa suna neman umarni na dindindin da zai tabbatar da mallakar gonakin da suka gada daga iyayensu.

Ya kuma jaddada cewa umarnin wucin gadi yana nan daram.

A nasa bangaren, lauya mai kare wadanda ake kara, Barrister Muhd Aminu Abdullahi, ya ce abokan huldarsa sun mallaki kasar ta hanyar bin ka’ida.

Ya kara da cewa kotun za ta saurari dukkan bukatar da ke gabanta ranar, 9 ga Yuli, 2026a ranar da zata sake zaman shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here