Share the post "Kudin Magada Naira Miliyan 35 Sun Bace a Hannun Ma’aikacin Kotu"
Iyalan wani mamaci sun roki hukumar kula da harkokin Shari,a ta Jihar Kano da ta kawo musu daukin gaggawa bayan da suka zargi cewar kudin gadonsu Naira Milyan 35 sun bace a hannun wani ma,aikacin, a Babbar Kotun Shari’ar Musulunchi dake Goron Dutse, cikin Birnin Kano.
Karanta Labari: Hukuncin Finland Kan Ekpa Sako ne ga Masu Daukar Nauyin Ta’addanci – Ministan Shari’a
Abba Inuwa, daya daga cikin ‘ya’yan mamacin, ya bayyana cewa bayan an siyar da shagon da ya rage daga kadarorin mahaifinsu, an tura kudin zuwa asusun wani ma’aikacin kotu mai suna Sadiq Mahmoud Sadiq, wanda shi ne mai kula da kudade a kotun, maimakon a tura su zuwa asusun gwamnati.
“Muna cikin matsanancin hali. Mun jira kotu ta raba kudin, amma har yanzu shiru. Kwanaki kadan bayan alkalin kotun ya umarci mu sakawa Magatakarda mai kula da harkokin kudi sai ya shiga wasan buya damu. Yana guje mana, alkalin kuma yana cewa kudin na hannunsa ne,” in ji Inuwa cikin damuwa.
Karanta Labari: Fiye da Fursunoni 53,000 na jiran shari’a a gidajen gyaran hali – NCoS
Iyalan sun ce sun bi duk matakan shari’a bisa tsarin rabon gado na Musulunci, amma yanzu suna fuskantar kalubale daga bangaren shari’a.
Sun roki Hukumar Kula da Ayyukan Shari’a (JSC), Babbar Jojin Kano , Mai Shari’a Dije Aboki, da Shugaban Alkalan Kotunan Musulunchi a Kano, Khadi Tijjani Yusuf Yakasai da su sa baki don karbo musu hakkinsu.
“Muna da hujja cewa ba a saka kudin a asusun gwamnati ba. Muna bukatar gaskiya. Muna bukatar adalci,” Inuwa ya kara da cewa.
“Muna matukar bukatar kudin a halin yanxu, saboda nemawa guda cikinmu wanda yake fama da lararu. Muna nema masa lafiya, a taimaka mana.”
Da yake mayar da martani, Daraktan Sashen Yada Labarai da Kididdiga na Kotun Daukaka Kara ta Shari’a a Kano, Muzammil Ado Fagge, ya ce ba shi da masaniya kan zargin, amma zai bincika gaskiyar lamarin.
“Ban san komai ba a yanzu, amma zan bincika in dawo da bayani,” in ji Fagge.
Ya bayyana cewa idan har abin da ake zargi gaskiya ne, to hakan babban keta doka ne a tsarin shari’a.
Ya kuma jaddada cewa sabon tsarin da Babban Khadi Tijjani Yusuf Yakasai ya kafa, ya haramta ajiye kudin gado a asusun kowa sai na gwamnati.
“A Kotun Daukaka Kara ta Shari’a, babu wani alkalin da ke da damar taba ko sisin kwabo daga kudin gado saboda tsarin biyan kudi ta hanyar E-payment,” in ji Fagge.
Ya tabbatar da cewa duk wani sabawa da wannan doka babban laifi ne, kuma za a gano gaskiyar lamarin.
Share the post "Kudin Magada Naira Miliyan 35 Sun Bace a Hannun Ma’aikacin Kotu"









