DIG Frank Mba ya yi murabus bayan shekaru 34 a aikin ‘yan sanda

0

…PSC ta gayyaci AIGs bakwai don tantancewa zuwa matsayin DIGs

Daga Wakilinmu

Mukaddashin Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, mai kula da horo da ci gaban ma’aikata a Hedikwatar ‘Yan Sanda, DIG Frank Mba, ya yi murabus bayan ya shafe shekaru 34 yana aiki.

Murabus din Mba ya zo ne tare da wasu manyan jami’an da suka yi ritaya bayan murabus din tsohon Babban Sufeton ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, da kuma nadin IGP Olatunji Rilwan Disu a matsayin shugaban rundunar.

A halin yanzu, Hukumar Kula Da Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC) ta gayyaci mataimakan manyan Sufeton ‘yan sanda (AIGs) guda bakwai domin tantancesu don daga likkafarsu zuwa matsayin Mukadassan Manyan Sufeton ‘Yan Sanda (DIGs), don shiga cikin tawagar shugabanci da za su yi aiki tare da sabon IGP.

Karanta Labari: Magidanci Mai Mata Biyu a Bauchi Ya Hallaka Dan Achaba Domin Samun Kudin Aure

AIGs da aka gayyata don daukaka sun hada da: Margareth Ochalla, Kenechukwu Onwuemelie, Ishiaku Mohammed, Zacharia Fera Achinyan, Zango Ibrahim Baba, Mohammed Abdul Sulaiman, da Umar Shehu Nadada.

A cewar PSC, ana sa ran manyan jami’an za su bayyana a ofishin hukumar yau Juma’a.

DIG Mba, wanda ya taba zama mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda da kuma kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ikko ya fara aikin dan sanda a watan Mayu 1992 a matsayin mai daukar horo. Ya yi fice tun daga farko inda ya kammala karatu da matsayi mafi kyau a fannin ilimi a makarantar horas da sabbin hafsoshin ‘yan sanda ta Wudil, a Kano

Mba, ya kasance daya daga cikin ‘yan Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA), ya samu digirin zama lauya daga Jami’ar Lagos sannan ya halarci Babbar Makarantar koyar da aikin Lauya ta Najeriya a Abuja. Daga baya ya samu digiri na biyu a fannin Lauya daga Jami’ar Dundee a Scotland.

Karanta Labari: Kano Ta Kaddamar da Tsarin Sufuri na Zamani Don Inganta Tsaro da Saukaka Harkokin Zirga-zirga

A tsawon shekaru, ya halarci shirye-shiryen kwararru na kasashen waje, ciki har da FBI National Academy a Quantico, Amurka, da kuma kwasa-kwasan jagoranci a Jami’ar Harvard da Jami’ar Oxford.

Mba ya wakilci Najeriya a ayyukan kasa da kasa, ciki har da aikin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Liberia tsakanin 2006 da 2007.

A cikin aikinsa, ya yi aiki a muhimman mukamai da dama a fannin ayyuka, bincike, gudanarwa da hulda da jama’a. Ya taɓa zama kwamandan yanki a Ajah da Festac a Lagos, kwamishinan ‘yan sanda a Jihar Ogun, kwamishinan ‘yan sanda mai kula da rundunar tsaron iyaka a Hedikwatar ‘Yan Sanda, da kuma AIG mai kula da FCID Annex, Panti, Lagos.

A cikin sakon bankwana, Mba ya nuna godiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa damar da ya ba shi na yin hidima ga kasa a lokacin mulkinsa.

Ya ce: “Ina matukar godiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa damar da ya ba ni na yi wa kasarmu hidima a lokacin mulkinsa. Amincewa da jagorancin rundunar ‘yan sanda da goyon bayan da aka bai wa hukumar a wannan lokaci sun kasance masu matuƙar muhimmanci.”

“Babban girmamawa ne a gare ni na bayar da gudummawa ta wajen tsaron da kwanciyar hankali na kasarmu.”

Ya kuma gode wa ‘yan Najeriya bisa goyon bayan da suka ba shi a tsawon shekaru 34 da ya yi a hidima.

Ya ce: “Ina son na yi godiya ta gaskiya ga mutanen Najeriya bisa amincewa, karfafawa da hadin kai da suka ba ni a tsawon shekaru 34 na hidima. Aikin ‘yan sanda aiki ne mai wahala amma mai daraja, kuma duk wata nasara da muka samu ta kasance ne saboda fahimta da goyon bayan ‘yan Najeriya. Na bar aikin da zuciya cike da godiya da alfahari saboda samun damar yin hidima.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here